Yan Sultan Film Factory ne suka fara takalar mu, Algaita Dub Studio Fan Sun kawo hujjojin su

 


Kalli cikakken bidiyon anan 



Ga hujjojinsu

Assalamu alaikum warahmahmatullah


Ga wani bayani Mai Muhimmanci Gareku masoya


Gaskiyar magana akwai abubuwa guda 4 da ya kamata ku sani dangane da zancen dake yawo a social media, kan cewa Algaita Dubstudio suna faɗa da wani Kamfanin.


1. Banbanceceniya:

dukkan rubuce-rubucen da kuke gani a wannan shafi masoya ne ke wallafawa, ba mu kai tsaye ba. Saboda wannan fans page ne na Algaita, ba official page na kamfanin Algaita Dubstudio ba. Idan kuka duba sunan shafin, zaku tabbatar (Sai dai ko idan mutum bai iya karatu ba). Don haka C.E.O na Algaita Dubstudio Buzo Danfillo (Buzo Bhai) bai ma san da wannan magana ba, domin har yanzu ba ta kai matsayin da za mu miƙa masa ita ba.


2. Mafarin Al'amarin:

Wannan kamfanin mai suna Sultan Factory da kuke gani a jikin wannan hoton mai alamar Lamba ta 2 ne ya fara zuwa ya yi mana maganganu marasa daɗi bayan mun wallafa wani ɗauka a page. Ga screenshot ɗin sa a sama zaku iya dubawa ku gani. Wannan kaɗai ya kamata a gane cewa sune suka fara shigowa al'amarin mu.


3. Maganganun Motivation:

Motivational speaking da muke wallafawa ba a yanzu muke ƙirƙirar su ba. A'a, wasu wallafaffu ne tun shekaru 3–4 da suka wuce; wasu daga cikin su daga shafin Buzo Danfillo (Buzo Bhai) wasu kuma daga shafin Mai Suburbuda suke. Ga screenshot ɗin wasu daga ciki, (Lamba ta 3) ku duba date ɗin da aka fara wallafa su zaku tabbatar. (Kawai dai shi mutum mara gaskiya kullum cikin tsarguwa yake ne)


4. Maganar Fassara Cinema Copy:

Wannan daram yake ba sauyi, domin mu aiki mai inganci muke so mu samar da bayar da gudummawa ga yaren mu na Hausa (Kuma ko yanzu muna ganin tasirantuwar abun). Saboda haka ba zamu yi wa Film fassarar na ga dama ba.


Note:

Mun yi wannan bayanin ne domin Jawo hankalin masoya dasu kwantar da hankalin su, duk wani rashin kunyar mara kunya su daina biye wa, duk wani wanda zai yace Algaita kaza da kaza ku ƙyaleshi kada ku tanka masa, saboda sai ya fi jin zafin ƙin mayar da martani.


Bayyanawa duniya gaskiya tun daga farkon abun, da kuma rufe bakin masu ƙoƙarin kawo ruɗani.


Su Kuma bloggers dake ta yaɗa abun wai ana faɗa da mai kamfanin Algaita Dubstudio to su ji tsoron Allah, har yanzu wannan magana ba ta kai ga Buzo Danfillo (Buzo Bhai) ba, kasancewar bata da wani muhimmanci ko kaɗan ko tasirin da ya kamata yasan ta ma.


Wannan shine, Allah ya sa mu dace Aameen.


✍️ Uthman British (British Bhai)





Comments