Sunusi Oscar 442 Yasha Zagi Da Yabo

 


Wannan shine bidiyon da sunusi oscar 442 ya yada har ya jawo masa zagi daga wasu yan kungiyar izala, kamar yadda kuka sani mallam lawan triumph ya futo yayi wasu maganganu a kwanakin nan, wanda ya nasabta manzon Allah da wasu abubuwa, jama'a dayawa sun yi tur da wannan fatawar tashi inda wasu kuma suka gaskata abunda ya fada wanda sukace ai malamin ya kawo hadisi.


Wannan dambarwar yana faruwa ne tsakanin kungiyar izala da kuma darika wanda wani sanannen malamin darika yayi raddi mai zafi akan haka, malamin da ake kira Prof. Ibrahim makari yace bai kamata ana nasabta manzon Allah da ire iren abun kazantar ba, hakan kamar cin mutunci ne da taba janibin manzon Allah S.A.W, inda yace ko kaine aka taba shaksiyyar ka bazaka ji dadi ba me yasa zaka taba na fiyayyen halitta.


Ta bangaren malam lawan triumph shima yayi martani inda yace baya kwan shi sai da zakara inda yace ga hadisi nan karara kuma duk wanda ya karyata hadisi to ya karyata maganar manzon Allah S.A.W.


Bayan yayi wannan maganar shine wani yayi masa raddi kamar yadda zaku gani acikin wannan bidiyon: inda shi kuma sunusi oscar yayi sharing na bidiyon kenan baya goyon bayan abun da mallam lawan triumph ya fada kenan hakan ya jawo magoya baya wasu suka danganta hakan da siyasa inda sukace daman tun can yan Kwankwasiyya basa son malamin saboda abunda ya taba fada akansu wasu kuma sai godiya suke da sanya albarka.


Shin me zaku iya cewa akan hakan?

Ga bidiyon


Ga hujjar cewa yayi sharing:



Comments