Wata Matashiya Ta Kwancewa Jaruma Samha M Inuwa Zani a Kasuwa
Wata Matashiya Ta Kwancewa Jaruma Samha M Inuwa Zani a Kasuwa
A yau an sake samun wani sabon hargitsi a dandalin sada zumunta, bayan wata matashiya ta fito karara ta kalubalanci fitacciyar jarumar Kannywood, Samha M Inuwa, akan wani bidiyo da ta wallafa a shafinta na TikTok/Instagram. Bidiyon da jarumar ta wallafa ya nuna wani salo da wasu suka bayyana da cewa "ba na tarbiyya ba," lamarin da ya haifar da cece-kuce a tsakanin masoyanta da masu sukar ta.
A cikin bidiyon, ana jin muryar wata waka ko magana da ke dauke da kalmomi masu tayar da hankali – wanda da alama bai yi wa wasu mabiyanta dadi ba. Amma abin da ya fi daukar hankali shi ne rubutun da jarumar ta yi a matsayin caption, inda ta rubuta: "Allah sa mu yi kyakyawar karshe."
Sai dai wannan kalma mai bayyana buri da addu’a ba ta yi wa wata matashiya dadi ba. A cewar matashiyar, jarumar tana nuna rashin gaskiya da nuna rashin tsoron Allah. Matashiyar ta ce:
"Kina wasa da Allah, ki gama taka dokar Shi sai kuma ki rubuta 'Allah yasa ki yi kyakyawar karshe'? Wait, are you for real girl? You have to work hard for it (kyakyawar karshe)."
Wannan tsokaci ya jawo cece-kuce sosai inda wasu suka goyi bayan matashiyar suna cewa jarumanmu da dama suna amfani da addini a fuska, amma a zahiri suna aikata abubuwan da suka sabawa koyarwar addini. Wasu kuma sun bayyana cewa kamata ya yi a dinga gyara tsakanin juna cikin mutunci da nasiha, ba da cin mutunci ba.
Har yanzu jaruma Samha M Inuwa ba ta mayar da martani kai tsaye ba kan wannan suka, amma wasu daga cikin masoyanta sun fito suna kare ta, suna mai cewa babu wanda ba ya kuskure kuma addu’a ba laifi ba ce – komai laifin mutum.
Wannan lamari ya sake tunatar da mu yadda dandalin sada zumunta ke zama wajen nuna ra'ayi da kuma yadda shahararrun mutane ke fuskantar matsin lamba daga mabiyansu. A karshe, yana da kyau mu dinga lura da abubuwan da muke wallafawa da kuma yadda muke bayyana ra’ayoyinmu domin kare mutuncin juna da kuma tabbatar da zaman lafiya a kafafen sada zumunta.
Shin kai/ke da kake karanta wannan, me kake ganin ya dace: a rika fadakar da mutane a bainar jama’a ko a boye a basu shawara ta sirri?
Comments
Post a Comment