Kinje Abuja Kin Bayar Sai Aka Baki Mota Inji Wani Matashi

 


Lallai rashin sani yafi dare duhu wani matashi ya tafka kwaba a karkashin comment din jaruma nadia Adamu daya daga cikin jaruman kanny yar asalin kasar Nijar.


Bayan da tayi posting din hoton wata sabuwar mota da ta saya shine yaje kasan comments dinta yayi mata reply da "Kema kin bayar a Abuja an baki mota kenan nadia, shegiya kannywood gidan yan balaja'u", hakan ne ya kara tabbatar da cewa shi wannan matashi lallai bai san wacece nadia Adamu ba


Bari in takaita muku zance nadia Adamu tana daya daga cikin yayan manyan masu kudi a kasar Nijar mahaifinta daya ne daga cikin masu karfin fada aji a kasar Nijar, kamar yadda a nan Nigeria zamu ce minister ko senate ko member to haka itama a kasar Nijar mahaifinta keda karfin fada aji.


Bawai ta shigo kannywood dan ta samu kudi bane a'a ta shigo ne dan neman suna saboda ko alokacin da take harkar gadan gadan, da kudin ta take aiki kuma ba irin kana nan aiki da akeyi a kannywood ba. Manyan aiki takeyi na fada aji.


Sannan ya manta cewa jarumar ta jima da juyawa kannywood baya, ta koma kasarsu ta ci gaba da gudanar da harkokinta acan, ta iya yuwuwa taga kamar harkar bai karbeta ba.


Wannan matashin ya tafka babban kuskure kuma ya fadi abunda bashida sani a kansa, wanda a rayuwarta ma bata da wata alaka da wasu da ke Abuja, saboda duk abunda take nema mahaifinta yana mata.


Fatan za'a kiyaye.

Comments