Asmee Wakili Taga Ta Kanta A Wajen Masoyan Nura M Inuwa.
Masoyan nura m inuwa sun tura sakon nuna bacin ransu akan wani bidiyo da aka ganshi tareda jaruma asmee wakili tana tsaye a bayan shi tana kwaikwayon wata wakarshi.
Masoyan nashi sun kalli abun kamar wata alaka ce ke kokarin shiga tsakanin mawakin da jarumar duba da yadda yanzu ake samun auratayya tsakanin yan masana’antar.
Wani mai suna al ameen pro yayi bidiyo da ya ja hankalin jama'a inda yake bayyana Ra'ayinshi akan yadda jarumar take yiwa mawakin kallon soyayya da kuma yadda fuskarta ke nuna soyayya karara, inda yace a matsayinshi na masoyinshi kuma masu supporting din amarya kuma uwargida Amina bazasu zuba ido suna ganin hakan na faruwa ba.
Abunda ta jawo wannan zargin shine ganin yadda jarumar ta rufe comment section din ta ta yadda babu wanda zai iya yi mata comment a kasan bidiyon, abunka da yan TikTok a take suka fassara abun zuwa wani abun har suke nuna bacin ransu, wasu ma gani suke nura ya wuce ajin kula mata irin su asmee wakili.
Lamarin na kara zafi inda wasu kuka daga cikin masoyan asmee wakilin sun fara mayar da martani sai dai har yanzu ita jarumar bata ce komai ba akan lamarin ga cikakken bidiyon anan
Comments
Post a Comment